Zamfara: Ƴan bindiga sun kashe ɗumbin jama’a’ a Anka da Bukkuyum

Rahotanni daga Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa ƴan bindiga sun kashe gwamman mutane a jihar.

Ƴan bindigar waɗanda suka je garuruwan Anka da Bukkuyum a kan babura masu ɗumbin yawa, sun afka ƙauyukan da ke ƙarƙashin waɗannan garuruwan inda suka rinƙa harbi kan mai uwa da wabi tare da cinna wa gidaje wuta.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa mutanen da ƴan bindigan suka kashe sun haura mutum 100. Wani wanda ya shaida lamarin ya shaida wa BBC cewa, ya ga gawa ta mutum takwas a wani ƙauye.

An bayyana cewa ƴan bindigan sun soma kai harin tun daga ranar Talata da dare har zuwa Laraba inda ƴan bindigan suka ci gaba da kutsawa daga wanan ƙauye zuwa wancan.

Har zuwa yanzu dai, ƴan sanda da sauran hukumomi a Jihar Zamfara ba su ce komai ba dangane da wannan hari.

Leave a Reply