Ƙungiyar Ƴan Jaridun Najeriya Ta Nemi Afuwar Gwamnan Jihar Katsina

Ƙungiyar Ƴan jaridun Najeriya ta nemi afuwar gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari bisa zarginsa da kama wani ɗan jarida da ke Abuja, Nelson Omonu tare da tsare shi.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a daren jiya, majalisar ta ce an yaudari wanda ke da alhakin kama Omonu kamar yadda aka yi masa a gidansa da ke Abuja ranar Asabar.

“Rikicin ya samo asali ne daga bayanan da ƴan uwa suka bayar, don haka ba manufar ƙungiyar NUJ ta babban birnin tarayyar Abuja ba ce ta kunyata gwamna da gwamnatin jihar Katsina.

Muna roƙon gafarar Gwamna Masari da gaske kuma muna rokonsa da ya amince da hakan a matsayin ɗaya daga cikin gazawar kokarin dan Adam,” wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Emmanuel Ogbeche da Ochiaka Ugwu, shugaba da sakataren majalisar.

Sai dai kuma Majalisar ta yi kira da a gaggauta sakin ɗan jaridar.

Leave a Reply