An Cafke Wata Matar Aure Da Ta Ke Safarar Ƴaƴan Cikinta Da Na Ƴan Uwanta Wurin Ƴan Bindiga

An cafke wata matar aure da ta ke kai ƴaƴan cikinta da na ƴan uwanta wurin ƴan bindiga a cikin daji inda suke yin lalata da su.

Matar ta bayyana yadda ta ke kai wa ƴan bindiga ƴaƴan nata da ƴaƴan ƴan uwanta ne bayan da rundunar ƴan sanda ta musamman kan yaƙi da ƴan fashin daji da ƴan ta’adda sun samu nasarar cafke ta tavna tsaka da wannan aika-aika.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, matar ta na yiwa ƴan bindigar safarar ƴan mata zuwa Dajin Galadimawa ana aikata alfasha da su.

Rundunar ƴan sandan ta IRT wadda Babban Sufeton Ƴan Sandan Najeriya ya kafa, ta titsiye matar inda ta bayyana yadda son zuciya ya rufe mata idanu ta shiga wannan harka.

Leave a Reply