Gwamnatin Jihar Kano Sun Yi Watsi Da sallar Jana’izar Bashir Othman Tofa

Jami’an gwamnatin jihar Kano sun yi watsi da sallar jana’izar Alhaji Bashir Othman Tofa a yau a gidansa da ke Gandu.

Ƙin halartar sallar jana’izar mamacin da gwamnatin jihar ta yi ya haifar da raɗe-raɗin cewa gwamnatin ta ƙi sakin bakin da ta yi wa marigayin.

Sallar jana’izar ta samu halartar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau da tsohon ministan noma da dai sauransu.

Tofa ya rasu ya na da shekaru 74 a safiyar ranar Litinin bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Shi dattijo ne kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a shekarar 1992, a ƙarƙashin rusasshiyar jam’iyyar Republican Party (NRC), Marigayin ya kasance mai sukar Gwamna Abdullahi Ganduje kan dokokin Masarautar Kano da suka mayar da tsohuwar Masarautar zuwa biyar a jihar.

Leave a Reply